‘Yan bindiga sun sake kai farmaki ga al’ummomin karkara a Ƙaramar Hukumar Mashegu ta Jihar Neja, inda suka kaƙaba musu harajin da ya kai Naira miliyan 10 tare da barazanar kai hare-hare idan ba a biya ba.

Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun bukaci al’ummomin Babban Rami da Kaboji su biya Naira miliyan biyu-biyu. Haka nan, an umarci mutanen yankin Sabon Rijiya da Sabon Rami su biya Naira dubu 500, yayin da ƙauyukan da ke kusa da Dajin Keji suka samu umarnin tara Naira miliyan 10 gaba ɗaya.

Bugu da ƙari, al’ummar ƙauyen Khizi ma sun samu umarnin biyan harajin Naira miliyan shida, tare da ba su wa’adin ranar Juma’a, 3 ga Oktoba, 2025, domin kammala biyan kuɗin.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BECHIHAUSA cewa lamarin ya jefa al’umma cikin fargaba:

“’Yan bindigar sun kashe mutane da dama kuma suna ci gaba da kai hare-hare. Sun kaƙaba haraji ga ƙauyukan da ke gefen dazukan Ibbi da gandun dajin Kanji National Park. Muna roƙon gwamnati ta gaggauta ɗaukar mataki, saboda yawancinmu manoma ne, kuma sama da kashi 90 cikin 100 na amfanin gona bai ma kai girbi ba,” in ji shi.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa da dama daga cikin manoma an kashe su ko an yi garkuwa da su a gonakinsu, yayin da matafiya ke fuskantar kwanton ɓauna a kan manyan tituna. Wasu ƙauyuka ma ‘yan bindigar na kona su gaba ɗaya a yayin hare-harensu.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version