Hukumar yi wa ƙasa hidima ta (NYSC) ta bayyana cewa tana samar wa gwamnatin jihar Legas da jama’arta hidima da kudinta ya kai darajar Naira biliyan 14 a kowace shekara.

Darakta Janar na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ne ya bayyana haka yayin ziyarar ban-girma da ya kai wa Gwamna Babajide Sanwo-Olu a fadar gwamnatin jihar da ke Marina, Legas.

Janar Nafiu ya ce sama da corps members 44,000 ke bayar da irin wannan gudunmawa a fannonin lafiya da ilimi da sauransu, ciki har da likitoci 333, masu magunguna 306, nas-nas 274, da malamai 7,188. Ya ce Legas ce cibiyar da yawancin matasa ke fi so saboda tsaro da damammakin aiki.

Ya jinjinawa gwamnatin jihar bisa gyare-gyaren da ta ke yi a sansanin wucin gadi na Iyana-Ipaja da kuma ginin sabon sansanin daukar mutum 10,000. Haka kuma, ya nemi gwamnatin jihar ta ba NYSC motar daukar marasa lafiya tare da ci gaba da tallafa wa shirin a sauran fannoni.

An kafa NYSC ne a shekarar 1973 a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Janar Yakubu Gowon, domin ƙarfafa haɗin kan ƙasa bayan yaƙin basasa. Shirin ya zama wajibi ga kowane ɗalibin jami’a da ya kammala karatu a Najeriya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version