Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa akalla mutane miliyan 24 masu shekaru tsakanin 20 zuwa 79 suna fama da ciwon suga a nahiyar Afirka. Rahoton ya nuna cewa rabin wannan adadi, kusan miliyan 12, ba su ma san suna da cutar ba, lamarin da ke ƙara haɗarin samun nakasa, rikicewar jiki ko mutuwa kafin lokaci. WHO ta yi gargadin cewa idan ba a dauki matakin gaggawa ba, yawan masu ciwon suga zai kai miliyan 60 nan da shekara ta 2050.

Daraktan WHO na yankin Afirka, Dr. Mohamed Janabi, ya ce wannan ƙaruwa tana da nasaba da sabuwar rayuwa ta zamani, rashin motsa jiki, yawaitar kiba, da kuma ƙarancin samun kulawa a asibitoci. Ya bayyana cewa ciwon suga kan iya lalata zuciya, koda, idanu da jijiyoyi, wanda hakan ke jefa iyalai da al’umma cikin tashin hankali da karin nauyin kashe kuɗin jinya.

Ya ce taken bikin Ranar Ciwon Suga ta bana shi ne “Diabetes Across Life Stages” wato ciwon suga ba ya barin kowa; yara, matasa, manya da tsofaffi na iya kamuwa da shi. Don haka ya ce ana bukatar kulawa daga matakin rigakafi har zuwa gano cuta da kula da ita na tsawon rayuwa. Ya kuma tunatar da cewa kasashen Afirka sun amince su daidaita tsarin yaki da cutar tun shekarar 2024.

Janabi ya ce WHO na tallafa wa kasashe wajen aiwatar da hanyoyin kula da marasa lafiya a matakin cibiyoyin kiwon lafiya na farko, musamman ta hanyar shirin WHO PEN da PEN-Plus da ake amfani da su a ƙasashe da dama. Ya bukaci gwamnati a nahiyar ta karfafa kasafin kudi ga cututtukan da ba sa yaduwa, da kuma haɗa yaki da ciwon suga cikin shirin lafiya na kasa domin kare rayuka da inganta lafiya baki daya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version