Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta bayyana cewa Indomie Noodles Vegetable Flavour da hukumomin Faransa suka janye daga kasuwa ba a samar da shi a Najeriya ba kuma ba a sayar da shi a ƙasar. Hukumar ta ce an janye samfurin ne a Faransa saboda gano sinadaran madara da ƙwai da ba a bayyana ba, wanda ka iya janyo matsalolin lafiya ga masu rashin lafiyar wasu abinci.
A cikin wata sanarwa da Darakta Janar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta sanya wa hannu ranar Lahadi, hukumar ta ce ta ɗauki matakan sa-ido a faɗin ƙasar domin hana yiwuwar shigo da wannan samfurin Najeriya. An umurci daraktocin yankuna da masu kula da jihohi da su ƙara tsaurara bincike, tare da kwashe samfurin nan take idan aka gano shi a ko’ina.
NAFDAC ta kuma jaddada cewa taliya (noodles) na cikin jerin kayan da aka haramta shigo da su ƙasar, abin da ya rage yiwuwar shigowar samfurin. Hukumar ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa duk Indomie da sauran nau’ikan taliya da ake sayarwa a ƙasar ana kera su ne a gida bayan cikakken bincike da tantancewa. Ta shawarci jama’a da su yi taka-tsantsan, su kai rahoto idan sun ga samfurin, tare da tabbatar da cewa NAFDAC na ci gaba da kare lafiyar al’umma.
