Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta cafke wata mata mai suna Shodunke Yetunde Simbiat, wadda ake zargi tana daga cikin manyan jiga-jigan wata ƙungiyar fataucin hodar iblis (cocaine) da aka tarwatsa tun da farko a jihohin Legas da Ogun. Kama Simbiat ya zo ne kusan watanni 20 bayan NDLEA ta tarwatsa wata babbar kungiyar fataucin kwaya da ma’aurata Bolanle Lookman Dauda da Olayinka Toheebat Dauda ke jagoranta, inda aka kwato kwayoyin da darajarsu ta kai biliyoyin naira.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana cewa bayan dogon bincike da sa ido, jami’an hukumar sun gano Simbiat mai shekaru 39 a matsayin mai ajiye kwayoyi ga ƙungiyar. An cafke ta ne a ranar 9 ga Disamba, 2025, a gidanta da ke Surulere, Legas, inda aka gano hodar iblis mai nauyin kilo 23.5 da aka ɓoye a ɗakin ‘ya’yanta, wadda darajarta a kasuwa ta kai sama da Naira biliyan 5. Simbiat ta amsa mallakar kwayoyin, kamar yadda hukumar ta tabbatar.
A gefe guda, NDLEA ta ce ta cafke wasu mutane a sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da filin jirgin saman Murtala Muhammed da kan iyakar Seme, tare da kwato tramadol, tapentadol da tabar wiwi a manyan adadi. Shugaban NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya yaba wa jami’an hukumar bisa ƙoƙarinsu, tare da kira gare su da su ƙara sa ido musamman a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara domin dakile safarar miyagun kwayoyi a fadin Najeriya.
