Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta sanar da janye, dakatarwa da kuma soke rijistar magunguna da kayayyakin lafiya guda 101 daga kasuwannin Najeriya sakamakon matsalolin tsaro, da rashin ingancin amfani da su. Hukumar ta ce wannan mataki na daga cikin shirinta na tabbatar da cewa al’umma na samun ingantattun kayayyakin lafiya da kuma kare lafiyar jama’a daga amfani da kayayyakin da ba su dace ba. Wannan mataki ya kuma nuna ƙudirin hukumar na yaki da magungunan bogi da na jabu da suka dade suna addabar tsarin kiwon lafiya na ƙasar.

Mai ba da shawara kan harkokin yada labarai na NAFDAC, Mista Sayo Akintola, ya bayyana cewa matakin janye kayayyakin ya biyo bayan gwaje-gwaje da kuma binciken da aka gudanar bayan fitar kayayyaki kasuwa (post-marketing surveillance) wanda ya gano cewa wasu daga cikin magungunan ba su cika ƙa’idojin hukumar ba. Ya ce, “Idan samfur ya gaza samun sinadaran da ake buƙata ko ya gaza cika ƙa’idar da aka shimfiɗa, hakan na iya zama barazana ga lafiyar masu amfani. Saboda haka dole ne a janye shi daga kasuwa domin kare lafiyar jama’a.”

Hukumar ta bayyana cewa wasu daga cikin kayayyakin da aka janye an mayar da su ne ta hanyar kamfanonin da ke da lasisin samarwa ko rarrabawa, bayan sun gano cewa lokacin amfanin magungunansu ya ƙare ko kuma sun kasa cika ƙa’idojin NAFDAC. Mista Akintola ya ce, “Wasu ‘yan kasuwa masu bin doka sukan kai rahoton irin waɗannan kayayyaki ga NAFDAC domin a lalata su ta hanya ta musamman. Wannan irin haɗin gwiwa na da matuƙar muhimmanci wajen kare masu amfani da magani da kuma tabbatar da gaskiya a harkokin masana’antar magunguna.”

Daga cikin magungunan da aka janye akwai Abacavir Sulfate/Lamivudine Dispersible Tablets (60mg/30mg), Amaryl M da Amaryl M SR Tablets, Aprovasc 150mg/5mg Tablets, magungunan zazzabin cizon sauro irin su Artemether/Lumefantrine 40mg/240mg da ASAQ (Artesunate Amodiaquine Winthrop) a nau’o’i daban-daban. Haka kuma akwai magungunan ido da hanci kamar Betopic Eye Drop, Iliadin Nasal Sprays, da magungunan ƙwayoyin cuta irin su Invanz 1g Injection, Penicillin G Sodium Sandoz da Sporanox 100mg Capsules. NAFDAC ta bayyana cewa waɗannan kayayyaki ba za a sake yarda a ƙera su, shigo da su, rarraba su, tallata su ko amfani da su a cikin Najeriya ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version