Majalisar Dokokin Jihar Benue ta amince da bukatar da Gwamna Hyacinth Alia ya gabatar mata domin ɗaukar rancen Naira biliyan 100 don aiwatar da manyan ayyukan ci gaban jihar. An amince da bukatar ne a zaman gaggawa da majalisar ta gudanar a ranar Juma’a 10 ga Oktoba, karkashin jagorancin Kakakin Majalisar, Alfred Emberga. A cikin wasikar da aka karanta ga ‘yan majalisar, Gwamna Alia ya bayyana cewa za a yi amfani da kuɗin wajen gyara da samar da kayan aiki a asibitoci 23, gina da gyaran makarantu na kimiyya, kammala ayyukan hanya da gada, gina cibiyoyin koyon sana’o’i da kuma kafa makarantu masu amfani da fasahar zamani a kowane mazabar tarayya a jihar.
Haka kuma, gwamnatin jihar na shirin amfani da wani ɓangare na rancen wajen gina da samar da kayan aiki ga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Benue (Benue State University of Agriculture, Science and Technology), da ke Ihugh. Bayan tattaunawa, majalisar ta amince da bukatar gwamnan gaba ɗaya tare da jaddada bukatar a yi amfani da kuɗin cikin gaskiya da rikon amana domin bunƙasa ci gaban jihar.
Sai dai Jam’iyyar PDP ta jihar ta nuna adawa da wannan mataki, tana bayyana shi a matsayin “rashin hankali da ganganci” musamman a wannan lokaci da jama’a ke fama da matsin tattalin arziki. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na jihar, Tim Nyor, ya fitar, PDP ta zargi gwamnati da rashin bayyana gaskiya da cikakken bayani game da rancen. Ta ce wannan lamari na iya jefa jihar cikin wani sabon yanayi na bashin da ba za a iya ɗauka ba.
PDP ta bukaci majalisar ta sake nazarin matakin da ta dauka tare da taka rawar gani a matsayin mai sa ido kan ayyukan gwamnatin jiha maimakon zama “ƴar amshin shata” ga duk wani shirin gwamnati. Jam’iyyar ta jaddada bukatar yin taka-tsantsan wajen ɗaukar irin waɗannan matakai don kauce wa matsalolin bashi da tasirin tattalin arziki ga jama’ar Benue.
