Wasu mayakan Boko Haram sun kai mummunan hari kan sansanin sojoji a Ngamdu, kusa da hanyar Damaturu–Maiduguri, a Karamar Hukumar Kaga ta Jihar Borno da safiyar Juma’a 10 ga Oktoba. Rahotanni sun nuna cewa harin ya auku ne da misalin ƙarfe 2:30 na dare, inda sojoji hudu suka rasa rayukansu, yayin da biyar suka samu munanan raunuka. Kakakin rundunar Operation Hadin Kai, Laftanar Kanar Uba Sani, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa.

Ya bayyana cewa sojojin Operation Hadin Kai sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan bayan wani gagarumin hari da suka kai, inda su ka yi amfani da makaman zamani kamar Rocket Propelled Grenades (RPGs), jiragen leƙen asiri masu ɗauke da bama-bamai, da kuma bama-baman da ake kunnawa ta na’ura (IEDs). Duk da ƙarfi da dabarun da mayakan suka yi amfani da su, sojoji sun tsaya tsayin daka suka mayar da martani da ƙarfin makami, inda suka yi wa ‘yan ta’addan mummunan rauni. Sai dai harin ya janyo asarar rayukan sojoji hudu da raunuka ga wasu biyar, tare da lalata wasu manyan motocin yaki.

Kanar Sani ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun shuka bama-bamai a kan hanyar Ngamdu–Damaturu domin hana isowar ƙarin dakarun taimako, lamarin da ya tilasta rufe hanyar na ɗan lokaci. Sai dai injiniyoyi na rundunar sojin sun gaggauta cire bama-baman guda uku, kuma an buɗe hanyar domin ci gaba da zirga-zirgar sojoji da fararen hula. Ya kara da cewa an sake samar wa dakarun kayan aiki da harsasai domin ci gaba da aikin tsaro a yankin.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa bayanai daga leƙen asiri sun tabbatar da cewa ‘yan ta’addan sun yi babban rashi, inda aka gano sun binne gawarwakin kusan mutane 15 a yankin Bula Wura kusa da Wasaram. A gefe guda, direbobin motoci sun tabbatar da cewa an samu cunkoso a hanya bayan harin, sakamakon binciken sojoji. Muktar Yahaya, jami’in Borno Express, ya ce motocinsu da dama sun makale saboda tsauraran matakan tsaro da aka ɗauka a yankin bayan harin.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version