Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa, NAFDAC, ta fara kona kayayyaki marasa inganci da suka kai darajar sama da Naira biliyan 20 a birnin Ibadan, jihar Oyo. A cewar hukumar, an gudanar da aikin ne a wajen zubar da shara na Moniya domin hana irin waɗannan kayayyaki dawowa kasuwa su haifar da illa ga lafiyar jama’a.

Daraktar Janar na NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, wacce mataimakiyarta, Mrs. Florence Uba ta wakilta, ta bayyana cewa kayayyakin da aka lalata sun haɗa da magunguna na jabu, kayan abinci marasa kyau, sinadarai masu haɗari, da kayan kwalliya da suka lalace. Ta ce an kwace kayayyakin daga masana’antu, ‘yan kasuwa, da kuma masu shigo da kaya daga waje, yayin da wasu kamfanoni masu bin doka suka mika nasu da suka lalace da kansu.

Farfesa Adeyeye ta gode wa Hukumar Kwastam wadda ta mika wa NAFDAC akalla kwantena 25 na kayayyakin da ta kama domin a lalata su. Haka kuma ta yabawa jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda, sojoji, DSS, da sauran hukumomi bisa goyon bayan da suke baiwa hukumar wajen kare lafiyar al’umma.

NAFDAC ta yi kira ga shugabannin al’umma, likitoci, malaman addini da ‘yan jarida da su taimaka wajen wayar da kan jama’a kan haɗarin siyan magunguna daga masu sayarwa ba bisa doka ba. Haka kuma ta bukaci jama’a su rika ba da rahoton duk wata shakka da suka samu kan magunguna ko kayan abinci domin a kare rayukan ‘yan ƙasa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version