Shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, ya garzaya kotun daukaka ƙara da ke Abuja domin neman ta hana Babbar Kotun Tarayya yanke hukunci a shari’ar ta’addanci da ake masa, wadda aka tsara za a kammala a ranar 20 ga Nuwamba. Kanu ya ce kotun ta farko ba ta da hurumin ci gaba da shari’ar saboda dokar da gwamnati ta dogara da ita wajen tuhumarsa — wato Terrorism Prevention and Prohibition Act — ta riga da ta lalace, don haka babu sahihin tuhuma a kansa.
A baya, mai shari’a James Omotosho ya ƙi amincewa da bukatar Kanu ta “no-case submission” inda ya nemi a watsar da karar gaba ɗaya, sannan ya ba shi dama sau da dama ya kare kansa. Sai dai Kanu ya ki kare kansa, yana mai cewa babu ƙa’ida ko tushe da ya kamata ya kare kansa a kai. A ƙarshe, alkalin ya ɗora ranar 20 ga Nuwamba domin yanke hukunci.
Kanu, wanda yanzu ya daukaka ƙara, ya nemi kotun dora tanka ta hana wancan hukuncin saboda a cewarsa, alkalin farko ya yi watsi da batun hurumin kotu da kuma sahihancin tuhumar gaba ɗaya. Ya kuma zargi kotun da gaza yin la’akari da umarnin kotun koli da ta ce wasu daga cikin tuhume-tuhumen da ake masa — musamman lamba ta bakwai — ba su da ƙarfi domin an riga an soke su a doka.
A cikin ƙarar da ya shigar mai sakin layi 13, Kanu ya yi gargadin cewa idan kotun daukaka ƙara ta bari a yanke masa hukunci, hakan zai zama zalunci kuma zai hana shi damar samun cikakken adalci. Ya ce gwamnati ba za ta yi wata hasara ba idan aka dakatar da yanke hukuncin, amma idan aka ci gaba, zai zama tamkar an hana shi damar kare kansa yadda doka ta tanada. Kotun daukaka ƙarar dai ba ta saka ranar sauraron wannan bukata ba tukuna.
