Rundunar Sojojin Najeriya ta ƙara zafafa hare-haren ta’addanci a faɗin ƙasar nan, inda ta kashe da dama daga cikin ‘yan Boko Haram, ISWAP da kuma sauran ‘yan bindiga cikin makonni biyu. Kakakin rundunar, Manjo Janar Olatokunbo Bello, ya bayyana cewa dakarun sun kuma kubutar da mutum 67 da aka yi garkuwa da su tare da cafke mutum 94 da ake zargi da aikata laifuka.

A Arewa maso Gabas, dakarun Operation Hadin Kai sun ci gaba da murƙushe maboyar ‘yan ta’adda a Borno da Adamawa, inda suka gano bindigogi masu yawa, manyan makamai, da kayan haɗa nakiya. Haka nan, an kama wasu masu ba da bayanai da tallafi ga ‘yan ta’adda, ciki har da masu kai musu kayan masarufi.

A Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, dakarun Operation Fagge Yamma da Operation Enduring Peace sun kashe ‘yan bindiga a Jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina, Kebbi, Kaduna da Plateau. Sun kuma kama barayi, masu sayar da makamai da kuma wani fitaccen ɗan ta’adda mai suna Ibrahim Wakili a Sanga, Jihar Kaduna, tare da ceto wasu mutanen da aka yi garkuwa da su.

A yankin Niger Delta, Operation Delta Safe ta lalata wuraren tace danyen mai na fasa ƙwauri, inda ta hana satar mai da darajarsa ta kai sama da N15.8m. Haka nan a Kudu maso Gabas, Operation Udo Ka ta kashe wani ɗan ta’adda tare da kama wasu bakwai a jihohin Imo, Enugu, Akwa Ibom da Cross River. Sojojin sun samu yabo daga hedkwatar tsaro bisa jajircewarsu wajen kare ƙasa da tabbatar da zaman lafiya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version