Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta fitar da sanarwar gargadi ga ‘yan Najeriya kan yaduwar kwaroron robar kariya ta “Kiss” a manyan kasuwanni a faɗin ƙasar. Sanarwar, wadda aka wallafa a ranar Litinin, 30 ga Disamba, 2025, ta ce an gano kayayyakin bogi a kasuwannin Onitsha, Idumota, Trade Fair, da wasu kasuwanni a Kano, Abuja, Uyo, Gombe da Enugu.
NAFDAC ta bayyana cewa bayanan sun fito ne daga DKT International Nigeria, wata babbar ƙungiya mai zaman kanta da ke aikin wayar da kai kan tsarin iyali da rigakafin cutar HIV/AIDS. Hukumar ta jaddada cewa kwaroron Kiss na asali ana amfani da su ne domin kariya daga ɗaukar ciki ba tare da shiri ba da kuma cututtukan da ake ɗauka ta jima’i.
Sai dai hukumar ta yi gargadin cewa nau’in bogin na da matuƙar haɗari ga lafiya, sakamakon rashin inganci, rashin tsafta, ƙarancin man shafawa da kuskuren bayanan lakabi. NAFDAC ta ce ta umarci ofisoshinta na jihohi da yankuna da su ƙara sa ido tare da cire kayayyakin bogin daga kasuwanni, tare da kira ga jama’a su rika sayen kayayyakin lafiya daga amintattun wurare kaɗai.
