Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana cewa kasar na bukatar akalla tan miliyan 25 na masara a duk shekara domin biyan bukatar abinci da kuma karfafa tsaron abinci a fadin kasa. Karamin Ministan Noma da Tsaron Abinci, Sanata Aliyu Abdullahi, ne ya bayyana hakan a wani taron tuntuba da jama’a da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a.

Abdullahi ya ce gwamnati na kara kokari wajen bunkasa noman cikin gida domin rage dogaro da shigo da abinci daga kasashen waje. Ya kuma ce matakan da ake dauka sun fara yin tasiri a kasuwa, inda farashin muhimman kayan abinci ya ragu da kusan kashi 50 cikin 100 a sassa daban-daban na kasar.

Ministan ya kara da cewa gwamnati ta bai wa bangarorin samar da shinkafa da masara da alkama muhimmanci domin samar da damammaki ga kananan manoma da sauran masu ruwa da tsaki. Ya ce ma’aikatar na daidaita manufofinta da ajandar “Renewed Hope” ta Shugaba Bola Tinubu domin tabbatar da cewa Najeriya na samar da abincin da take ci tare da cin abin da take samarwa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version