Wani rahoton Daily Trust ya bayyana cewa Najeriya ta kashe har N12.8 tiriliyan wajen shigo da man fetur daga Agusta 2024 zuwa Oktoba 2025, duk da yunƙurin ƙara inganta tacewa a cikin gida. Hukumar NMDPRA ta ce an shigo da fiye da lita biliyan 15.4, inda a watan Satumba 2024 aka fi yawan shigo da man saboda rashin tacewa a gida.

Rahoton ya nuna cewa duk da fara samar da man Dangote Refinery tun Satumba 2024, har yanzu ƙasar na dogaro sosai ga shigo da mai, inda manyan watanni sun kai fiye da biliyan 1.3. A ɓangaren tacewa, Dangote ya samar da lita biliyan 7.2 cikin watanni 15, amma yana fuskantar tsaiko na vessel clearance, lamarin da ya rage hanzarin fitar da kayayyaki.

A wata wasika da kamfanin ya aikewa NMDPRA, Dangote ya ce a shirye yake ya rika samar da lita biliyan 1.5 a wata daga Disamba, da kuma 1.7 biliyan daga Fabrairu 2026. Ya kuma roƙi a ba shi cikakken goyon baya don tabbatar da isasshen mai ga ‘yan Najeriya. Bechi Hausa ta lura cewa masana na ganin hanin shigo da mai yanzu zai iya haifar da monopoly, wanda zai iya kawo barazana ga tsaron makamashi.

Masana kamar Henry Adigun da Prof. Wumi Iledare sun ce Najeriya ba za ta iya daina shigo da mai ba yanzu saboda ƙarancin masana’antun tacewa. Sun ce Dangote na taka rawa wajen rage dogaro da waje, amma har yanzu akwai ƙalubale irin su tsadar man fetur, jinkirin sufuri, karancin iskar aiki, da kuma barazanar mamaye kasuwa. Sun ba da shawarar a kula da farashi, yawan tacewa, da ingancin hanyoyin jigilar man don tabbatar da tsaron makamashi a ƙasa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version