Hukumar DSS ta damke wani likita da ake zargin yana kai wa ’yan bindiga kayan magani a dazukan Jihar Kwara. An kama shi ne a Jebba bayan bayanan sirri sun nuna cewa ana jigilar magunguna daga Sokoto don jinyar ’yan ta’adda da suka sami raunuka. Rahotanni sun ce da dama daga cikin su na dauke da harbin bindiga daga arangama da jami’an tsaro.
Hukumar tsaro ta bayyana cewa ’yan bindigar da suka ji raunuka na iya kai wa cibiyoyin lafiya hari domin neman magani. Jami’in tsaro ya shawarci hukumomi da su tsaurara matakan tsaro a asibitocin da ke cikin dazuka ko yankunan karkara. Wannan mataki yana daga cikin kokarin da ake yi domin katse hanyoyin samun tallafi da ke taimaka wa masu garkuwa da mutane.
Bechi Hausa ta tattaro daga ofishin Gwamnan Kwara cewa wannan kamun babban ci gaba ne a yunkurin kawo karshen ayyukan ta’addanci a yankin. CPS din Gwamna, Rafiu Ajakaye, ya ce nasarar DSS ta sake tabbatar da cewa hukumomin tsaro suna rufe duk wata kafa da ke karfafa ayyukan ’yan bindiga. Ya kara da cewa gwamnati na kara hada kai da jami’an tsaro domin dakile duk wata hanyar taimaka wa masu garkuwa da mutane.
Gwamnatin jihar ta yi alkawarin ci gaba da bai wa hukumomin tsaro goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya. Ana kuma gargadin ma’aikatan lafiya da su rika taka-tsantsan da duk wata ziyara ko bukatar da aka kawo cikin yanayi mai barazana. Jama’a an bukace su rika bayar da bayanan sirri cikin hanzari idan suka ga duk wani motsi da ba su yarda da shi ba.
