A ranar Jumma’a, 5 ga Disamba 2025, TikTok ta bayyana cewa za ta bi dokar Ostireliya wadda za ta fara aiki 10 ga Disamba, wadda ta haramta wa masu ƙarancin shekaru shiga kafafen sada zumunta. Dokar ta fara ne domin kare matasa daga illolin kafofin sada zumunta, inda kamfanoni za su fuskanci tara har zuwa dala miliyan 32 idan suka ƙi bin umarni.

TikTok ta ce duk wanda bai kai shekara 16 ba za a toshe shafinsa, yayin da sauran matasa masu asusu za su samu sanarwa cewa an kashe account ɗinsu. Haka kuma, duk wani abin da suka wallafa a baya ba zai sake bayyana ga jama’a ba. An ba matasan damar daukewa ko share bayanansu, ko su jira har su kai shekara 16 su dawo.

A cikin sanarwar da TikTok ta fitar, kamfanin ya bayyana cewa matasan da aka toshe za su iya nuna shaidar shekaru ta hanyar hoton fuska, katin shaidar gwamnati ko hanyar biyan kuɗi. TikTok ta shawarci iyaye su tattauna da yaransu kan muhimmancin bayyana gaskiyar shekarunsu.

Sai dai ƙungiyar kare haƙƙin fasaha ta Digital Freedom Project ta shigar da ƙara a kotu domin dakatar da dokar, tana cewa tana takura ‘yancin faɗar albarkacin baki. Kasashen Malaysia da New Zealand suma sun nuna sha’awar daukar irin wannan mataki nan gaba. Wannan ya nuna yadda duniya ke ƙoƙarin shawo kan matsalolin da ke tattare da amfani da kafafen sada zumunta tsakanin matasa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version