Tsohon sanata Kabiru Garba Marafa ya bayyana goyon bayansa ga barazanar shugaban Amurka Donald Trump na yiwuwar shiga Najeriya don kawar da ‘yan ta’adda. Marafa ya ce wannan gargadi zai tilastawa gwamnati ta dauki tsauraran matakai kan tsaro. Ya fadi haka ne a hirarsa da Politics Today na Channels TV a jiya Laraba. Ya ce batun kare rai shi ne gaba da komai.

Marafa ya ce ba ya tare da masu cewa barazanar Trump beta hakkin Najeriya ne, domin inji shi, “meye amfanin ‘yancin ƙasa idan ana mutuwa ba dare ba rana ?” Ya kara da cewa maganganun Trump sun sake jawo hankalin duniya kan hare-haren da ake kai wa al’ummar Kirista. Tun bara Trump ya umurci Pentagon da fara shirin kai farmaki a Najeriya. Ya kuma yi barazanar katse tallafin Amurka idan kashe-kashen suka ci gaba.

A cewar Marafa, matsayar Trump ta kara matsa wa hukumomin Najeriya lamba su nuna aiki kan matsalar tsaro. Amurka ta sanya Najeriya a jerin kasashen da ake zargi da tauye ‘yancin addini. Wannan mataki ya kara jefa Najeriya cikin muhawarar kasa da kasa kan tsaro. Marafa ya ce dole gwamnati ta fifita kare rayuka fiye da duk wani abu.

Trump dai ya ce zai iya aika runduna domin kawar da ‘yan ta’adda da ya kira masu kai hari ga Kiristoci. Yace duk wani yunkuri na Amurka zai kasance mai “gaggawa, zafi, kuma mai tsauri.” Marafa ya sake nanata cewa idan gwamnati ta gaza, sai dai duniya ta matsa mata. Ya ce yanzu lokaci ne da dole a dauki matakin da zai tabbatar da tsaro a dukkan fadin kasar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version