Gwamnatin Najeriya na iya samun har Naira tiriliyan ɗaya duk shekara daga sabon harajin ribar jarin (CGT) na kashi 30% da ake shirin fara aiwatarwa a Janairu 2026. A shekarar 2024 an samu ribar da ta kai kusan N956.2 biliyan daga cinikin hannayen jari na N2.8 tiriliyan, wanda harajin zai bayar da N286.8 biliyan. A rabin farkon 2025 kuwa, an kai ciniki na N4.19 tiriliyan, wanda ke nuna yiwuwar samun harajin kusan N995 biliyan idan kasuwa ta ci gaba da wannan hanzari.

Sai dai masana harkokin kasuwa sun gargadi cewa irin wannan babban kaso na haraji zai iya rage kwarin gwiwar masu zuba jari, musamman manyan kamfanoni da masu hannun jari na waje. Sun ce tsarin zai iya janyo fitar jarin kasashen waje (capital flight) zuwa kasuwannin da ke da rangwamen haraji, kamar Kenya da ke da 0%, Ghana 15%, da Morocco 10%, yayin da Masar ma ta soke nata harajin. Wannan bambanci na iya rage sha’awar zuba jari a kasuwar hannayen jarin Najeriya.

Haka kuma, masana kamar Patrick Ajudua da Amaechi Egbo sun nuna damuwa kan rashin tsayayyen bayani a cikin dokar — musamman yadda za a tantance sake zuba jari da yiwuwar a dora haraji kan ribar da aka tara kafin dokar ta fara aiki. Sun bayyana hakan a matsayin rashin adalci da zai iya rage amincewar masu zuba jari da sa kasuwar ta zama mara tabbas.

David Adonri na Highcap Securities ya bayyana harajin a matsayin mataki da zai iya rage cinikayya, raunana kasuwa da takura samun jarin dogon lokaci da ake bukata don farfado da tattalin arzikin Najeriya. Ya bukaci gwamnati ta sake nazarin tsarin, ta tsara shi cikin salo mai jawo jarin cikin gida da na waje, maimakon matakin da zai iya karya ci gaban kasuwar hannayen jari da ake kokarin ingantawa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version