Hukumar NDLEA ta kama wata ’yar ƙasar Brazil mai shekaru 30, Ingrid Benevides, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, da hodar iblis kilo 30.09 da aka ɓoye cikin kwalayen kofi. An kama ta ne a ranar Juma’a, 23 ga Janairu, 2026, bayan ta iso Abuja daga Doha ta jirgin Qatar Airways.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya ce bincike ya nuna cewa kwalayen kofi guda 21 da ke cikin jakunkunan ta na ɗauke da hodar iblis da darajarta ta haura biliyan ₦3. Ya ce wannan ita ce hodar iblis mafi girma da aka taɓa kamawa a filin jirgin Abuja, inda wacce ake zargin ta ce ta shigo Najeriya ne a matsayin yawon shakatawa.

A wani lamari makamancin haka, NDLEA ta kama wasu matafiya biyu a filin jirgin Lagos da ke kan hanyarsu zuwa Turkiyya da kwayoyin tapentadol da tramaking. Haka kuma, jami’an hukumar sun kwace kilo 1,848 na tabar wiwi a Tekun Lekki, tare da kama wasu mutane da ake zargi da safarar abubuwan fashewa da miyagun ƙwayoyi a jihohi da dama.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version