An samu rikici tsakanin Majalisar Wakilai da Ƙungiyar Ƙananan ’Yan Majalisa (Minority Caucus) kan binciken da ake yi game da zargin sauya dokokin haraji na ƙasa. Shugaban kwamitin binciken na ƙananan ’yan majalisa, Afam Ogene, ya yi gargaɗin cewa watsi da rahoton kwamitinsu na wucin-gadi zai ƙarfafa rashin ladabi da raunana martabar Majalisar Dokoki.
Ogene ya yi wannan jawabi ne bayan mataimakin kakakin Majalisar, Philip Agbese, ya bayyana rahoton a matsayin wanda “lokaci ya riga ya wuce,” bayan fitar da kwafin dokokin haraji na hukuma. Ya ce rahoton nasu bai zargi Majalisar Wakilai ba, sai dai ya nuna yunkurin da wasu suka yi na tauye ’yancin Majalisar wajen gudanar da aikinta.
Sai dai kakakin Majalisar Wakilai, Akin Rotimi, ya mayar da martani inda ya ce matakin da ƙananan ’yan majalisa suka ɗauka ya saɓa ƙa’ida kuma ba shi da hurumin doka. Ya jaddada cewa kwamitin da Majalisa ko Kakakin Majalisa suka kafa kaɗai ke da ikon bincike, yana mai cewa har yanzu kwamitin haɗin gwiwa ƙarƙashin Muktar Betara na ci gaba da aikinsa kan batun dokokin haraji.
