Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta kama wata ‘yar kasuwa mai shekaru 35, Rabi Muhammad, bisa zargin ɓoye ƙwayoyin tramadol guda 3,200 a cikinta na ƙarya domin fitar da su zuwa ƙasar Benin. An cafke matar ne a ranar 16 ga Fabrairu, 2026 a iyakar Seme Border, bayan jami’ai sun lura cikinta ba na gaske ba ne, inda bincike ya gano ta ɗaure kwalbar calabash mai ɗauke da ƙwayoyin a cikinta.
Haka kuma a ranar, jami’an hukumar sun kama wani ɗan ƙasar Ivory Coast mai suna Michael Gohouri a Mallam Aminu Kano International Airport, yayin da yake ƙoƙarin tafiya Milan ta Addis Ababa. Binciken na’ura ya nuna ya haɗiye miyagun ƙwayoyi, inda daga bisani ya fitar da ƙunshi 82 na hodar iblis mai nauyin kilo 1.49, wanda aka ce zai kai Turai domin samun kuɗi Yuro 5,000.
hukumar ta kama wani attajiri kuma shugaban kamfanin gine-gine, Kolapo Oladapo Raji, a Legas, inda aka samu kilo 89.2 na tabar wiwi mai ƙarfi a gidansa. Jami’an sun ce mutumin ya amsa cewa ya shiga harkar fataucin miyagun ƙwayoyi ne bayan samun riba mai yawa daga hulɗar da yake yi da wasu abokan hulɗarsa na ƙasashen waje.
Hukumar NDLEA ta ce waɗannan kamen na daga cikin matakan da take ɗauka domin dakile fataucin miyagun ƙwayoyi ta filayen jiragen sama da kan iyakoki. Ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da tsaurara matakai domin gurfanar da duk masu hannu a irin waɗannan laifuka, domin kare lafiyar al’umma da martabar ƙasar nan.


