Jam’iyyun adawa da suka haɗa da ADC da NNPP da PDP sun kaurace wa zaɓen cike gurbi na majalisar dokokin jihar Kano da aka gudanar a Ungogo da Kano Municipal. Jam’iyyun sun ce sun janye ne saboda zargin tafka magudi da kuma tsoron tashin hankali, inda suka zargi tsarin zaɓen da karkata zuwa ga jam’iyyar APC.

Shugaban ADC na Kano, Musa Ungogo, ya ce jam’iyyarsu ta guji shiga zaɓen ne domin tabbatar da zaman lafiya musamman a watan Ramadan. Shi ma shugaban PDP na jihar, Yusuf Kibiya, ya ce sun kai ƙorafi ga INEC amma ba su samu amsa ba, yana mai cewa za su nemi mafita a kotu.

A gefe guda kuma, APC ta lashe zaɓen cike gurbi na majalisar dokokin jihar Rivers, inda aka ayyana Napoleon Ukalikpe da Burabari Loloo a matsayin waɗanda suka yi nasara. Hukumar zaɓe ta ce zaɓen ya gudana cikin lumana, yayin da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yabawa yadda aka gudanar da shi cikin kwanciyar hankali.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version