Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da kashe wani babban kwamandan Boko Haram mai suna Abdullahi Mafa, yayin ci gaba da hare-haren da take kai wa a jihohin Borno da Adamawa. Mai magana da yawun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba, ya ce an kashe Mafa ne a yankin kogin Visik, karamar hukumar Madagali, inda aka kuma kwace bindigar AK-47 da alburusai.

Bugu da ƙari, rundunar ta kama wani da ake zargi mai suna Dauda Usman Gubula, wanda ake tuhumar samar wa ‘yan ta’adda jirage marasa matuƙa da suke gyarawa don kai hare-hare. An samu jirage marasa matuƙa guda biyu a hannunsa, tare da kayan haɗinsu da kuma na’urar bayar da wuta ta hasken rana guda 20.

Sojojin sun ce wannan nasara wani muhimmin mataki ne wajen raunana ƙarfin Boko Haram a yankin, tare da tabbatar da tsaro ga al’ummar jihohin da suka yi fama da hare-haren ‘yan ta’adda a baya. Wannan aiki na ci gaba da nuna jajircewar sojojin Najeriya wajen dakile ayyukan Boko Haram.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version