Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta karɓi ‘yan Najeriya 147 da suka makale a ƙasar Libya, bayan haɗin gwiwa da ƙungiyar International Organisation for Migration (IOM) da sauran hukumomi. Wadannan ‘yan ƙasa sun iso Najeriya ne a ranar Talata da yamma, ta filin jirgin sama na Murtala Muhammed International Airport, Lagos, cikin jirgin Air Libya mai lambar rajista 5A-BAE.

A cewar NEMA, cikin waɗanda suka dawo akwai manya 100 (mazaje 32 da mata 68), yara 34 (mazaje 18 da mata 16) da kuma jarirai 13 (mazaje 5 da mata 8). Bayan isowarsu, jami’an hukumar shige da fice (NIS) sun gudanar da rajista da tantance su ta hanyar fasahar kwamfuta, domin tabbatar da sahihancin bayanansu da kuma shirya musu hanyoyin komawa cikin al’umma cikin sauƙi.

Hukumar ta bayyana cewa an ba wa waɗanda suka dawo taimakon gaggawa kamar abinci da ruwan sha, kula da lafiyar gaggawa, da kuma tallafin sufuri da shawarar kwantar da hankali. Wannan, a cewar NEMA, na cikin tsarin gwamnatin tarayya na tabbatar da dawowar ‘yan ƙasa cikin mutunci da tsaro.

NEMA ta gode wa hadin kan IOM, Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira da Masu Hijira (NCFRMI) da sauran abokan hulɗa wajen tabbatar da nasarar aikin. Hukumar ta ce za ta ci gaba da tabbatar da cewa kowanne ɗan Najeriya da ke ƙasashen waje cikin mawuyacin hali ya samu damar dawowa gida cikin aminci da kulawa ta ɗan adam.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version