Shugaban ƙungiyar IPOB da aka haramta, Nnamdi Kanu, ya kori dukkan mambobin tawagar lauyoyinsa yayin zaman kotu da aka gudanar a yau Alhamis. Kanu ya sanar da kotu cewa shi kansa zai kare kansa ba tare da wakilcin kowane lauya ba, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a zauren shari’a.
Bayan wannan sanarwa, babban lauya Kanu Agabi (SAN) wanda ke jagorantar tawagar lauyoyin ya bayyana cewa su ma sun yanke shawarar janyewa daga ci gaba da wakiltar Kanu a shari’ar. Wannan ya bar Kanu shi kaɗai a cikin akwatin masu laifi yana kare kansa kai tsaye.
A lokacin da ya ke magana daga cikin akwatin, Kanu ya kalubalanci kotu cewa ba ta da hurumin ci gaba da sauraron shari’arsa, yana mai cewa an karya ka’idar shari’a wajen gurfanar da shi a gaban kotun.
Wannan ci gaban ya ƙara tayar da hankula a cikin shari’ar da ta jima tana jan hankali, wadda ke da nasaba da tuhumarsa kan ayyukan da ake zargin ƙungiyar IPOB da aikatawa a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.
