Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wasu maza biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta same su da laifin kashe wani sabon ango a wani harin fashi da makami da suka kai da dare. Wadanda aka yankewa hukuncin su ne Aliyu Hussaini da Amir Zakariyya, mazauna Sheka Sabuwar Abuja da Unguwar Malam a Karamar Hukumar Kumbotso.
Mai shari’a Amina Adamu-Aliyu ta ce masu gabatar da kara sun tabbatar da laifin tuhumar da ake musu ba tare da wata shakka ba, tana mai bayyana harin a matsayin mai muni da tayar da hankali. Lauyan gwamnati, Lamido Abba-Sorondinki, ya shaida wa kotu cewa lamarin ya faru da misalin karfe 2:47 na daren 11 ga Yunin 2025, inda suka kai wa marigayin Yazid Haruna hari da wukake da adda tare da kwace wayoyi biyu da N19,500.
Kotun ta same su da laifin hada baki, fashi da makami da kuma kisan kai, duk da cewa sun musanta zargin tare da neman sassauci. An yanke musu daurin shekara guda kan hada baki, daurin rai da rai kan fashi da makami, sannan hukuncin kisa ta rataya kan kisan kai, bayan an same su da laifi karkashin sashe-sashen dokar Penal Code ta Jihar Kano.


