Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta bayyana cewa an samu ci gaba a shirin saka mitoci, inda kwastomomi 187,765 suka samu mita a fadin kasar nan cikin watannin Satumba da Oktoba 2025. Rahoton da NERC ta fitar ya nuna cewa an saka mitoci 80,943 a Satumba, sannan 106,822 a Oktoba, lamarin da ya daga yawan masu mita daga kashi 55.37 cikin 100 zuwa 56.07 cikin 100 a watan Oktoba, duk a cikin shekarar 2025.
Rahoton ya kara da cewa yawan kwastomomin wutar lantarki masu aiki ya karu zuwa 12,071,018 a Oktoba, yayin da adadin wadanda ke da mita ya kai 6,768,386, inda har yanzu fiye da mutane miliyan 5.3 ke karbar kudin wuta ta kiyasi. Kamfanonin rarraba wuta na Ikeja da Eko ne suka fi samun nasara wajen saka mitoci, da kaso 85.59 da 84.75 cikin 100, yayin da wasu kamfanoni kamar Yola, Jos, Kaduna da Kano suka kasa kaiwa kashi 35 cikin 100.
Duk da wannan ci gaba, NERC ta soki wasu kamfanonin rarraba wuta kan jinkirin saka mitoci da kin mayar da kudin da kwastomomi suka biya tun da dadewa. A cewar NERC, akwai mitoci sama da 600,000 a kasar nan da ba a girka ba, tare da kira ga kamfanonin da su kara kaimi. Wannan rahoto, wanda aka fitar a ranar Lahadi, 14 ga Disamba, 2025 da misalin karfe 12:00 na dare, na nuna cewa idan aka ci gaba da wannan tsari, Najeriya na iya kusantar cimma burin saka mita ga kowa nan ba da jimawa ba.
