Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, ya yi kira da a janyo jami’o’in Najeriya masu zaman kansu su shiga Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU). A cewarsa, dole ne a samu haɗin kai tsakanin dukkan jami’o’i domin tabbatar da ingantaccen tsarin ilimi a ƙasar.

Ajaero ya bayyana haka ne a lokacin tattaunawar da aka gudanar da shugaban ASUU, Farfesa Christopher Piwuna, a shirin Toyin Falola. Ya ce lokaci ya yi da za a daina cin zarafi da raina mambobin ASUU, yana mai nuna takaici kan yadda gwamnati ta kasa cika yarjejeniyar da ta sanya hannu tun daga shekarar 2009.

Shugaban NLC din ya ce tun farko an ƙirƙiri ASUU ne domin raba ta da NLC, inda aka hana ta zama ƙarƙashin tsarin ƙwadago, amma daga baya ƙungiyar ta kai ƙara kotu ta kuma samu nasara. Ya ce hakan na nuna cewa ASUU na da cikakken haƙƙin zama cikin tsarin kare muradun ma’aikata.

Ajaero ya ƙara da cewa ƙirƙirar jami’o’in masu zaman kansu an yi shi ne domin karya ƙarfafa muradin ASUU, don haka dole ne a fara tattaunawa da shugabannin waɗannan jami’o’i domin su shiga cikin ƙungiyar. Ya ce yin hakan zai ƙara ƙarfi wajen kare martaba da ingancin ilimi a matakin jami’a a faɗin ƙasar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version