Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta yi kakkausar suka kan ficewar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar, inda ta bayyana matakin a matsayin rashin mutunta al’ummar da suka ba shi gagarumin goyon baya a zaɓen gwamna na shekarar 2023.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Ladipo Johnson ya fitar, NNPP ta ce ficewar gwamnan tamkar cin amanar al’ummar Kano ne, waɗanda suka zaɓe shi bisa dogaro da biyayyarsa da dogon zamansa a tafiyar siyasar Kwankwasiyya tsawon shekaru da dama.
Jam’iyyar ta yi gargaɗin cewa matakin na iya jefa jihar hannun masu adawa da ci gabanta, tare da kiran magoya bayanta a Kano da su kwantar da hankalinsu, su bi doka, tare da kaucewa duk wani abu da zai iya haddasa rikici ko tayar da hankula a siyasance.
