Jami’an tsaro na NSCDC a Jihar Kogi sun cafke wasu yara ƙananan guda 21 da ake zargin anyi safarar su daga jihohin arewa zuwa Kogi ba bisa ka’ida ba. An kama su ne a yankin Yagba East, bayan samun sahihin bayanan sirri daga wasu mafarauta da suka gano wani motsi da basu yarda da shi ba.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an yi zargin cewa waɗannan yara na kan hanyarsu ta shiga wani ɓoyayyen tsarin daukar matasa domin horar da su cikin harkar ta’addanci. Jami’an NSCDC tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun kama manyan mutane da suka raka yaran, waɗanda ba su iya bayar da tabbataccen dalilin jigilar su ba. An kuma gano wasu abubuwa da suka haifar da ƙarin damuwa kan tsaron yankin.

A cewar rahoton da Bechi Hausa ta tattaro, Gwamna Ahmed Usman Ododo ya bayar da umurnin a mika yaran ga Ma’aikatar Harkokin Mata da Walwalar Jama’a domin kula da lafiyarsu. Yaran kuma za a mika su ga gwamnatocin jihohinsu bayan kammala bincike da tantance su.

Gwamnatin Kogi ta jaddada cewa za a gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a safarar yaran, bisa dokokin jihar na kare haƙƙin yara. Haka kuma ta sha alwashin ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro da al’umma don tabbatar da cewa ba a bar wata kafa ga miyagun ayyuka a cikin jihar ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version