Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar, ya yi watsi da ƙarfi da tasirin tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo da ake cewa yana da shi a harkar zaɓe, yana mai cewa bai iya lashe jiharsa ko yankin Kudu maso Yamma a zaɓen shugaban ƙasa na 1999 ba.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da ’yan jarida ranar Laraba, a daidai lokacin da takaddamar kalamai tsakaninsa da Obasanjo ta sake kunno kai. Ya ce Arewa ce ta taimaka wa Obasanjo ya zama shugaban ƙasa a shekarar 1999.

Rikicin ya ƙara tsananta ne bayan Obasanjo ya bayyana zaɓen Atiku a matsayin mataimakinsa a 1999 a matsayin “babban kuskuren” da ya yi a  mulkinsa, tare da zargin tsohon mataimakin nasa da rashin biyayya da hannu a wani yunƙurin tsige shi. Atiku ya yi watsi da wannan bayani, yana zargin Obasanjo da sauya tarihin abubuwan da suka faru domin amfanin siyasa gabanin 2027.

Atiku ya kuma ce ya taimaka wajen gina tsarin siyasar da ya ba su damar samun nasara a 1999, tare da ƙirƙirar damarmaki ga matasa yayin da yake mataimakin shugaban ƙasa. Ya yi alkawarin cewa idan aka zaɓe shi a 2027, gwamnatinsa za ta ci gaba da samar wa matasa damarmaki na riƙe mukaman shugabanci.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version