Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya yi gargaɗin cewa jam’iyyar PDP za ta lalace idan gwamnoninta suka ci gaba da watsi da shi daga muhimman shawarwarin jam’iyyar. Yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, Wike ya bayyana takaicinsa kan yadda ake ware shi daga tattaunawa da yanke shawara, duk da irin rawar da ya taka wajen gina jam’iyyar.
Wike ya ce ba wai jam’iyyar APC bace ke haddasa matsalolin PDP ba, illa dai kuskuren da shugabannin jam’iyyar ke yi da kansu. Ya yi zargin cewa wasu gwamnonin jam’iyyar suna son mamaye harkokin PDP ta hanyar amfani da kuɗaɗen gwamnati, abin da ya kira “hanyar lalata jam’iyyar daga ciki.” Ya kuma bayyana cewa idan aka shirya babban taron jam’iyyar ba bisa ka’ida ba, to ba zai halarta ba, sai dai idan an bi doka da tsarin jam’iyya.
A gefe guda, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kira ‘ya’yan jam’iyyar da su hada kai don sake gina PDP a gabannin babban taron jam’iyyar da za a gudanar a Ibadan a watan Nuwamba. Ya ce duk da matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta, PDP na da damar dawo da mulki a 2027 idan shugabanninta suka fifita hadin kai da gaskiya a kan son zuciya.
Sai dai a yankin Arewa maso Yamma, wasu dattawan PDP sun zargi Ministan Tsaron Ƙasa, Mohammed Bello Matawalle, da tilasta wa magoya bayan PDP komawa jam’iyyar APC ta hanyar amfani da mukamai da dukiya. Sun ce wannan lamari na iya lalata tsarin dimokuraɗiyya da kuma raunana jam’iyyar adawa a shiyyar Arewa maso Yamma, suna roƙon Shugaba Bola Tinubu da ya ja kunnen ministan.
