Jam’iyyar APC ta fuskanci sabon rikici game da makomar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima gabanin zaɓen 2027, bayan cire hotonsa daga wata babbar fosta a taron jam’iyyar da aka gudanar a Maiduguri, Jihar Borno. Lamarin ya faru ne yayin taron sauraron ra’ayoyi kan gyaran kundin tsarin jam’iyyar a yankin Arewa maso Gabas.

Fostar ta nuna hotunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnonin APC biyar na yankin da kuma mai ba jam’iyyar shawara kan shari’a, amma ba a saka hoton Shettima ba duk da kasancewarsa ɗan Borno. Wannan ya janyo zanga-zanga daga Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdulkarim Lawan, wanda ya bayyana lamarin a matsayin rashin adalci da kuma abu mai tayar da hankali a daidai lokacin da bai dace ba.

Kusan irin haka ta faru a Gombe a 2025, inda aka ambaci Tinubu a matsayin ɗan takarar APC na 2027 ba tare da ambaton Shettima ba. Duk da APC ta ce rade-radin cire Shettima daga tikitin 2027 ba gaskiya bane ƙirƙira ne, wasu jiga-jigan jam’iyyar a Borno sun yi gargadin cewa irin wannan kuskure na iya haddasa rarrabuwar kai da raunana haɗin kan jam’iyyar gabanin babban zaɓe.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version