Wani rikici da ya ɓarke a ƙauyen Kangire na ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Jihar Jigawa, tsakanin manoma da makiyaya ya yi sanadin jikkatar mutane shida. Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya ɓarke ne bayan zargin makiyaya da kutsawa gonaki tare da lalata amfanin gona. Wannan lamari ya sake tayar da hankalin al’umma a yankin.
Wata sanarwa da Ishak Ibrahim Fanini, mai magana da yawun shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Muhammad Uba, ya wallafa ta tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce shugabancin ƙaramar hukumar ya shiga tsakani domin sasanta tsakanin ɓangarorin biyu. Ya kuma ja kunnen cewa ba za su amince da duk wata fitina ko wani abu da zai tayar da hankulan jama’a ba.
A wajen taron sulhun da aka gudanar, an jaddada muhimmancin kauce wa rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya, lamarin da Bechi Hausa ta bibiyi domin gano tushen matsalolin da ke tayar da tarzoma a yankunan da ke fama da irin waɗannan rikice-rikice. Wannan ba shi ne rikicin farko ba a Jigawa, domin a watan Oktoba an samu mutuwar mutane uku a wani rikici makamancin haka a Birniwa LGA.
Masana sun danganta yawan rikice-rikicen ga sauyin yanayi, fari, da matsalolin tattalin arziki da suka tilasta yawancin makiyaya komawa kudancin yankuna domin neman ciyawa da ruwa. Wannan hijira na haifar da matsaloli a yankunan noma, inda ake samun babban ɓarna ga gonaki da kuma tada jijiyoyin wuya tsakanin al’ummomin yankin.
