A Kano, a daren Juma’a, 30 ga Nuwamba 2025, misalin ƙarfe 11 na dare, rundunar Operation MESA ta 3 Brigade ta gudanar da samame a Tsanyawa, inda ta ceto mutane bakwai da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su. Wannan na zuwa ne bayan kiran gaggawa daga mazauna Yankamaye Cikin Gari da suka yi zargin harin ’yan bindiga a yankin.
Sanarwar da Kakakin Rundunar Sojin Najeriya, Captain Babatunde Zubairu, ya fitar yau Lahadi ta bayyana cewa sojoji tare da haɗin guiwar Jirgin Sama da ’Yan Sanda sun isa wajen cikin gaggawa, suka yi musayar wuta da maharan, suka kuma kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su. Sai dai kafin isowar jami’an tsaro, maharan sun kashe wata mata ’yar kimanin shekaru 60.
Zubairu ya ce bayan harin farko, sojoji sun bi sahun ’yan bindigar zuwa yankin Rimaye, inda suka ci gaba da harbi mai ƙarfi wanda ya tilasta wa maharan barin mutanen da suke tsare. Bechi ta tattaro cewa duk da nasarar wannan aikin, mutane huɗu daga cikin wadanda aka sace har yanzu ba a gano su ba, lamarin da ya tayar da hankalin al’ummar yankin.
Rundunar ta ce maharan sun gudu zuwa kan iyakar Kankia a Jihar Katsina, inda ake ci gaba da bin diddigin su. Kwamandan 3 Brigade ya yabawa dakarun bisa jarumta, tare da kira ga jama’a su rika taimaka wa hukumomin tsaro da sahihan bayanai domin tabbatar da kawar da ’yan bindiga daga yankunan iyaka.
