Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bukaci a samar da dokokin da zasu taimaka wajen amfani da kafafen sada zumunta a Najeriya sakamakon yadda ake ta yin barna da su. Ya bayyana haka ta bakin Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, yayin taron Ulama na Arewa da aka gudanar a Kaduna kan matsalolin tsaro da tattalin arziki. Ya nuna damuwa kan yadda mutane ke amfani da kafafen sada zumunta wajen zagi da bata suna ba tare da tsoro ko ladabtarwa ba, yana mai cewa kasashe da dama suna da tsare-tsare da ke hukunta masu yada kalaman batanci ko tada rikici.
Shugaban Majalisar Shari’a ta Kasa, Dr. Bashir Aliyu Umar, ya jaddada cewa taron na da nufin hada kan al’umma da samar da mafita ga kalubalen yankin. Ya gargadi jama’a kan yada labaran karya a kafafen sada zumunta, yana mai cewa hakan na kara rura wutar rikici da rashin jituwa. Ya bukaci mutane su rika amfani da kafafen sadarwa ta hanyar da za ta taimaka wajen gano tushen matsalolin tsaro da magance su.
Shahararren malamin addini, Sheikh Ahmad Gumi, ya bukaci masu amfani da kafafen sada zumunta su kiyaye iyaka wajen yin mu’amala da juna, tare da neman aiwatar da dokokin da suka riga suka wanzu na kare mutunci da hana bata suna. Ya yi gargadin kada a yi tsauraran matakai na takaita kafafen sadarwa gaba ɗaya, amma ya nemi da a daidaita dokokin da zamani.
Taron ya samu halartar manyan malamai, shugabannin siyasa da masu ruwa da tsaki daga sassan Arewa. Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, ya bukaci al’umma su daina jingina laifin matsalar tsaro ga gwamnati kawai, yayin da wasu wakilai suka yi alkawarin hada kai wajen aiwatar da shawarwarin taron domin inganta zaman lafiya da cigaban kasa.
