Allah ya yi wa fitaccen malamin addini, Sheikh Usman Kusfa Zaria wanda aka fi sani da Rigi-rigi, rasuwa a daren jiya Lahadi a jihar Kaduna. Rasuwarsa ta janyo alhini a tsakanin al’umma da mabiyansa.

Rahotanni sun nuna cewa malamin ya rasu ne bayan fama da gajeriyar jinya. An ce ya rasu a asibitin sojojin Najeriya na 44 da ke Kaduna.

Sheikh Usman Kusfa ya rasu yana da shekara 57, inda ya bar matansa huɗu da ƴaƴa 37. Marigayin ɗan asalin garin Kusfa ne da ke Zaria a jihar Kaduna.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version