Kotun Koli ta tabbatar da ikon shugaban kasa na bayyana dokar ta-baci a jihohi domin hana hargitsi ko faduwar doka. Hukuncin ya ce shugaban kasa na iya dakatar da Zababben gwamna, mataimakinsa ko majalisar jiha na wani lokaci kadan yayin wannan yanayi.
Hukuncin ya biyo bayan karar da jihohin PDP suka shigar kan ayyana yanayi na gaggawa a Rivers, inda aka dakatar da gwamnan jihar da yan majalisun su na watanni shida.
Duk da haka, daya daga cikin alkalai ya nuna sabanin ra’ayi, inda ya ce shugaban kasa na iya ayyana dokar ta-baci, amma ba zai iya dakatar da zababbun shugabanni ba.
