Alhaji Aliko Dangote, shugaban kamfanin Dangote Industries Limited, ya yi kira da a binciki ayyukan hukumar NMDPRA, inda ya zargi shugabanta da yin galaba ga ‘yan kasuwar mai na waje da masu shigo da mai don kawo cikas ga masana’antar mai a Najeriya. A taron manema labarai a masana’antar Dangote Petroleum Refinery, Dangote ya tabbatar da cewa farashin man fetur (PMS) zai sauka zuwa N740 a lita daya daga gobe, farawa daga jihar Legas, sakamakon rage farashin gantry zuwa N699 a lita daya. Ya ce hakan zai fara aiki ne a tashoshin MRS.

Dangote ya bayyana damuwa kan ci gaban bangaren man fetur na kasa, inda ya ce dogaro da shigo da mai na waje yana kawo illa ga masana’antar cikin gida da kuma rage sha’awar zuba jari. Ya ce an bayar da lasisin shigo da man fetur na kusan lita biliyan 7.5 na kwata na farko na 2026, duk da isasshen karfin masana’antar cikin gida. Haka kuma, ya ce karancin sabbin masana’antar mai da kuma ci gaba da bayar da lasisin shigo da mai na waje na rage karfin masana’antar cikin gida.

Ya kara da cewa, masana’antar Dangote za ta ci gaba da tallafawa ‘yan Najeriya ta hanyar samar da man fetur mai inganci da araha, inda ya bayyana cewa, duk wanda ya zabi ci gaba da shigo da mai duk da isasshen mai daga cikin gida zai fuskanci sakamakon hakan. Dangote ya kuma bayyana niyyarsa ta baiwa ‘yan Najeriya damar mallakar hannun jari a masana’antar, domin kowa ya samu rabo a harkar man fetur.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version