Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya sauka daga muƙaminsa bayan kusan shekaru goma yana jagorantar hukumar.

A yayin taron da ya gudanar da kwamishinonin INEC a Abuja ranar Talata, Yakubu ya sanar da cewa ya mika ragamar shugabanci ga babbar kwamishina, May Agbamuche, wadda za ta rike mukamin shugaba a matsayin riko har sai an naɗa sabon shugaban hukumar.

Agbamuche ita ce kwamishinar da ta fi kowa dadewa a hukumar, abin da ya sa aka zabe ta don ci gaba da tafiyar da ayyuka a wannan lokaci na sauyin jagoranci.

Yakubu ya hau kujerar shugabancin INEC a Oktoba 2015, kuma an sake tabbatar da nadinsa a 2020. Ya jagoranci manyan zaɓukan 2019 da 2023, inda ya zama ɗaya daga cikin shugabannin INEC mafi dadewa a tarihin Najeriya. Saukarsa na zuwa ne yayin da ake jiran shugaban ƙasa ya naɗa sabon shugaban hukumar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version