Dakarun Operation HADIN KAI sun dakile yunkurin ‘yan ta’adda na kutsa kai yankin Bitta da ke Jihar Borno daga tsaunukan Mandara, inda suka kashe da dama daga cikinsu. Lamarin ya faru ne da misalin 12:30 na tsakar daren Alhamis, 19 ga Disamba, 2025, bayan dakarun sun gano motsin maharan ta hanyar na’urorin sa ido na zamani.
Rahotanni sun ce dakarun sun bari ‘yan ta’addan su kusanto cikin tazara mai dacewa kafin su kaddamar da farmakin kare kai cikin tsari, lamarin da ya yi sanadin hallaka wani babban jagoran ‘yan ta’adda da mai daukar bidiyonsa. Yayin da sauran suka yi yunkurin tserewa, bangaren rundunar sama ya kai hare-haren daidai-da-wuri, inda ya tarwatsa hanyoyin tserewarsu tare da kara raunana karfinsu.
Bayan fafatawar, dakarun kasa sun kwato makamai da kayayyakin yaki da suka hada da bindigogin AK-47, na’urar daukar bidiyo, rediyo na hannu, harsasai, wayoyi, bindigogin PKT da GPMG, da babura. A cewar Bechi Hausa, an kuma gano alamun jini da kaburbura marasa zurfi, alamar karin asarar da ‘yan ta’addan suka yi, yayin da rundunar ta jaddada kudurinta na murkushe ta’addanci da dawo da zaman lafiya a Arewa maso Gabas.
