Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin Naira tiriliyan 58.18 na shekarar 2026 a gaban Majalisar Tarayya, inda ya ware Naira tiriliyan 5.41 ga ɓangaren tsaro, wanda ya zama mafi girman kaso a kasafin kuɗin shekarar.

Tinubu ya bayyana cewa ba tare da tsaro ba, tattalin arziki ba zai bunƙasa ba, yana mai cewa kuɗaɗen za su taimaka wajen sabunta sojoji, ƙarfafa aikin ‘yan sanda bisa bayanan sirri, tsaron iyakoki da haɗin gwiwar hukumomin tsaro, tare da sabon tsarin yaƙi da ta’addanci a faɗin ƙasar.

Shugaban ƙasar ya kuma ayyana dukkan ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, kungiyoyin makamai da masu tallafa musu a matsayin ‘yan ta’adda, yana mai cewa wannan mataki ne domin rufe giɓin doka da ya bai wa masu tayar da hankali damar ci gaba da addabar ‘yan ƙasa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version