Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe wani babban kwamanda a kungiyar Boko Haram tare da wasu mayakan kungiyar 10 a wani samame da ta kai a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana cewa Abu Khalid ne babban kwamandan Boko Haram na biyu a dajin Sambisa.

Sanarwar ta kara da cewa Abu Khalid ya taka rawa wajen kitsa hare-hare da dama da mayakan Boko Haram suka kai a yankin. Najeriya dai ta shafe lokaci tana fuskantar hare-haren masu ikirarin jihadi a sassa daban-daban na kasar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version