Dakarun Sojojin Najeriya sun dakile jigilar kayayyakin tallafi da ake zargin na Boko Haram/ISWAP ne a Jihar Borno, bayan sun tare wata mota a kan hanyar Maiduguri–Bama. Aikin ya gudana ne a Jumma’a, 19 ga Disamba, 2025, bayan makamancin wannan nasara da sojoji suka samu kwanaki kalilan kafin hakan. Kakakin Operation Hadin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba, ya tabbatar da lamarin a wata sanarwa da aka fitar a Lahadi, 21 ga Disamba, 2025.
Sanarwar ta ce sojojin 25 Brigade sun kuma gano wasu bama-bamai (IED) a kan hanyar Damboa–Komala a ranar 17 ga Disamba, inda suka lalata su cikin nasara domin tabbatar da tsaro ga matafiya da jami’an tsaro. A wani samame daban, sojojin da ke bakin aiki a mashigar bincike ta Maiduguri–Bama sun kama wata mota mai lambar Legas dauke da kayan abinci da lemun kuzari, waɗanda ake zargin ana shirin kaiwa ’yan ta’adda a yankin Kirawa, karamar hukumar Gwoza.
A yayin samamen, an kama mutane biyu, tare da kwato kayan abinci iri-iri, wayoyin salula uku, kati, zobe, da kuɗaɗe a Naira da CFA. Bechi Hausa ta ruwaito cewa rundunar soji ta jaddada kudirinta na katse hanyoyin samun kayan tallafi ga ’yan ta’adda, tare da tabbatar da cewa an mika waɗanda aka kama da kayan da aka kwato ga sashen leƙen asiri domin zurfafa bincike, a wani yunkuri na ƙarfafa tsaro a Arewa maso Gabashin Najeriya.
