Rundunar Sojin Najeriya na shiyya ta 6 ta sanar da cafke wasu mutane 14 da ake zargi da satar mai, tare da kwace sama da lita 20,000 na man da aka sace a yankin Niger Delta. Hakan ya biyo bayan jerin samame da sojoji suka kai har tsawon makonni biyu a wuraren da ake zargin barayin ke gudanar da ayyukansu a boye.
A cikin samamen, sojoji sun rushe matatun mai guda 14 a wasu yankuna na Rivers, Abia, Delta, Akwa Ibom da Bayelsa. A Rivers da iyakokin Imo River, an lalata matatan mai shida tare da kwace ganguna da kwantena cike da mai da aka tace ba bisa ka’ida ba. Hakazalika, an gano buhuna 42 dauke da kusan lita 1,250 na man da aka sace daga wata rijiyar mai mai zaman kanta.
A Delta, sojoji sun cafke mutane uku a yankin Ughelli, tare da kwace lita 4,000 na man condensate, sannan a Warri an gano tanderun hada mai da buhuna masu dauke da man fetur na sata. A Akwa Ibom kuwa, an kama wata babbar mota tana sauke man dizal daga wani rumbun boye a Ikot Ekpene, yayin da a Bayelsa suma sojoji suka ci gaba da sintiri domin takaita satar arzikin kasa.
Kwamandan Division 6, Manjo Janar Emmanuel Emekah, ya yaba wa dakarun bisa aikin da suka yi, tare da umartar su ci gaba da matsa lamba kan masu barna da masu lalata tattalin arzikin kasa. Ya ce rundunar za ta kara hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da cewa ba a sake samun irin wadannan ayyuka ba a yankin.
