Mazauna yankin Gaza sun bayyana cewa dakarun Isra’ila sun janye daga arewa maso yammacin birnin Gaza zuwa gabashin yankin, a wani mataki da ke nuna sauyin dabarun sojin ƙasar.
Mai magana da yawun Firayim Ministan Isra’ila ya tabbatar da janyewar, yana mai cewa rundunar za ta koma zuwa wasu wurare da aka amince da su, domin samun damar mallakar kashi 53 cikin 100 na yankin zirin Gaza.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya kuma tabbatar da wannan mataki, yana mai cewa dakarun za su koma “wurin da aka amince da shi” bisa tanadin yarjejeniyar tsagaita wuta da ake aiwatarwa a halin yanzu.
Daftarin yarjejeniyar da Amurka ta gabatar wa Hamas da Isra’ila ya nuna cewa wannan shi ne matakin farko na tsagaita wutar da za ta kai ga sakin fursunonin Isra’ila daga hannun Hamas, da kuma sakin Falasɗinawa daga gidajen yarin Isra’ila. Yarjejeniyar na kuma nufin samar da zaman lafiya mai ɗorewa da kawo ƙarshen rikicin da ya daɗe yana ci a yankin.
