Sojojin rundunar sojin ƙasa na shiyya ta 6, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, sun samu manyan nasarori a yaki da sata da lalata bututun mai a Niger Delta. Daga ranar 23 ga Nuwamba zuwa 28 ga Disamba, 2025, sojojin sun kama mutane 19 da ake zargin masu sata ne, sun rufe gidajen bunkering 22, sannan sun kwato fiye da lita 180,000 na mai da aka sace na kimanin Naira miliyan 150.
A jihar Bayelsa, an rufe wani sansanin sarrafa mai a Siebu Creek da ke Ogbienbiri, inda aka gano babban tanki da ke ɗauke da lita 75,000 na mai da aka sace. A sauran wurare kamar Biseni da Okarki, an rufe gidajen bunkering da dama, an kwato mai fiye da lita 22,000, ciki har da gano babban jirgin Cotonou da aka loda da sacks 37 na mai sacewa.
A jihar Rivers, sojoji sun gano sacks 350 na mai da aka sace a Ogale, yayin da aka lalata gidajen bunkering biyu a Okarki Forest tare da kwato lita 3,000. A Delta da Akwa Ibom, an kama motoci da mutane suna satar mai da AGO, an kuma kwato fiye da lita 48,000 na kayayyakin sacewa. Janar Emmanuel Eric Emekah ya yabawa sojojin, yana mai kira ga al’umma su ci gaba da tallafawa hukumomin tsaro wajen kare muhimman wuraren ƙasa.
