Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia, ya ce rashin ilimi, talauci, rashin aikin yi, rashin daidaito, raunin hukumomi, rikice-rikicen addini da ƙabilanci, rashin kyakkyawan shugabanci da durƙushewar ɗabi’u na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa matsalar tsaro a Najeriya.
Alia ya bayyana hakan ne yayin gabatar da muƙala a taron Yakubu Gowon University da aka gudanar a Abuja. Ya ce hare-haren Boko Haram, ƴan bindiga, garkuwa da mutane da rikicin makiyaya da manoma sun yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi tare da barazana ga tsaron ƙasa.
Gwamnan ya jaddada cewa inganta ilimi mai inganci da adalci, horar da malamai, bunƙasa koyon sana’o’i da ƙarfafa hukumomin gwamnati na daga cikin hanyoyin magance tushen matsalar tsaro. Ya ce ilimi na taimakawa wajen rage tsattsauran ra’ayi, talauci da rashin aikin yi, tare da gina al’umma mai zaman lafiya da ci gaba.
