Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma sanatan da ke wakiltar mazaɓar Sokoto ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya, Aminu Waziri Tambuwal, ya sauya sheƙarsa zuwa African Democratic Congress (ADC) bayan ficewarsa daga Peoples Democratic Party (PDP). Tambuwal ya sanar da matakin ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
A cikin saƙon, Tambuwal ya ce matakin komawa ADC ya samo asali ne daga ra’ayinsa cewa Najeriya na buƙatar wani sabon ƙarfin siyasa da zai ginu kan gaskiya da haɗin kai da riƙon amana, tare da jajircewa wajen bunƙasa ƙasar.
Ya kuma jaddada ƙudurinsa na ci gaba da yi wa Najeriya hidima tare da tsayawa kan manufofin dimokuraɗiyya da haɗin kan ƙasa, bayan ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da saɓanin shugabanci da rabuwar kai a PDP ne suka sa ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar.


