Babban ɗan adawa daga jam’iyyar haɗaka ta ADC, Sanata Dino Melaye, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa har yanzu ‘yan Nijeriya na ci gaba da mutuwa sakamakon yunwa da tsadar rayuwa da manufofin gwamnati suka haifar.

Melaye, wanda ya taɓa zama ɗan majalisar dattijai, ya bayyana cewa Tinubu bai cika ko ɗaya daga cikin alƙawurran da ya ɗauka wa al’umma lokacin yaƙin neman zaɓe ba.

Ya kuma zargi shugaban ƙasa da almubazzaranci da kuɗaɗen gwamnati, ta hanyar siyan jirgin ruwa mai tsadar gaske, jirgin sama danƙarere, da kuma motar alfarma, a daidai lokacin da yawancin ‘yan ƙasa ke fama da talauci.

Melaye ya ce wannan lamari ya nuna rashin daidaito tsakanin abin da gwamnati ke faɗa da yadda take gudanar da mulki, yana mai kiran Tinubu da ya mayar da hankali kan ceto rayukan talakawa maimakon shagulgulan kashe kuɗi.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version